Bakonmu a Yau
Tattaunawa da Dr Kabiru Ibrahim Matazu kan faro taron yanayi na COP27 a Masar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:26
A rana ta biyu da fara taron duniya game da sauyin yanayi da ake kira Cop27 da ke gudana yanzu haka a Sharm el-Sheikh na Masar, Gidauniyar Bill Gates attajirin Amurka ta sanar da ware dala bilyan daya da milyan 400 a matsayin tallafi ga manoman Afirka da Kudancin Asiya.Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Kabiru Ibrahim Matazu, na jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, wanda da farko ya yi karin bayani a game da girman matsalar sauyin yanayi musamman ga bangaren noma a kasashen yammacin Afirka.