Isa ga babban shafi

An bude taron sauyin yanayi na COP27 a Masar

An bude taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya mai taken COP 27 a kasar Masar, a daidai lokacin da ake kira ga kasashe mawadata da su biya diyar kudade ga takwarorinsu matalauta, sakamakon yadda suka haddasa aukuwar musibu masu nasaba da sauyin yanayin.

Taron COP27 a Masar zai fi mayar da hankali wajen tara kudaden yaki da matsalar sauyin yanayi.
Taron COP27 a Masar zai fi mayar da hankali wajen tara kudaden yaki da matsalar sauyin yanayi. REUTERS - SAYED SHEASHA
Talla

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai tada hankali ya ce, shekaru takwas da suka shude na baya-bayan nan, sun zama mafi samun dumamar yanayi a tarihi, inda aka samu tumbatsar tekuna, narkewar tsaunukan kankara , tsananin zafi da dai sauran ibtila’o’in da ke nuni da sauyin yanayi.

Sakatere Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ya ce, a daidai lokacin da aka bude taron  na COP27, wannan doran duniyar da muke rayuwa a kai, na aikewa da mummunan sako.

A ‘yan watanni da ssuka gabata, ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a kasashe irinsu Pakistan da Najeriya, sannan matsalar fari ta yi kamari a nahiyar Afrika da Amurka, yayin da kuma guguwa ta yi shara a yankin Caribbean, inda kuma aka samu wani irin zafi mai tsanani da ba a taba gani ba a nahiyoyi uku na duniya.

Taron na COP27 da ke gudana a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh da ke kasar Masar, na zuwa ne a daidai lokacin da ake gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine, al’amarin da ya haddasa hau-hawan farashin kayyaki a sassan duniya.

Taron na bana zai fi mayar da hankali ne kan yadda za a tara kudaden tunkarar matsalar ta sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.