Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dubban mutanen da ake zargin 'yan ta'adda ne ke tsare a gidajen yarin Najeriya

Wallafawa ranar:

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar akwai kimamin fursunoni dubu 61 da ake zargin ‘ya ’yan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci, wadanda ke tsare a gidajen yarin da ke shiyyar Arewa maso gabashin kasar.

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP
Talla

Ministan harkokin cikin gida na kasar, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a lokacin ziyarar da ya kai gidan yarin Kirikiri da ke jihar Lagos, bayan harin da aka kai gidan yarin Kuje da yayi sanadiyar kubutar da mambobin kungiyar Boko Haram sama da 60.

Da dama daga cikin ‘yan uwan wadanda ake tsare bisa wanccan zargi dai sun muna rashin gamsuwar su da hakan, kamar yadda Ibrahim Burma Abdullahi daya daga cikin wadanda aka tsare da ‘yan uwan sa, ya bayyana a zantawar sa da Khamis Saleh.

Sai a latsa alamar sautin da ke sama domin sauraron tattaunawa tsakanin Ibrahim Burma Abdullahi da Khamis Saleh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.