Sakataren MDD ya ziyarci cibiyoyin gyaran halin tubabbun Boko Haram
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:36
A cigaba da ziyarar da sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a yankin Sahel game da abinda ya shafi ‘yan gudun hijira da kuma tashe-tashen hankalin da ake fuskanta, a ranar Talata ya ziyarci wasu daga cikin cibiyoyin gyara hali na tubabbun mayakan Boko Haram da ke jahar Borno a tarayyar Najeriya, inda ya yaba da kokarin da gwamnatin jahar ke yi wajen dawo da su cikin al’umma.
Dangane da hakan ne muka tuntubi kwamishinar ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jahar Hajiya Zuwaira Gambo, ga abinda ta ke cewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu