Sakataren Harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana yarjejeniyar zaman lafiyar da Israila da kulla da wasu kasashen Larabawa da aka yi wa suna Abraham Accord‘ a matsayin wanda bai ci karo da yunkurin sasanta rikicin Israila da Falasdinu ba.
Yayin da yake jawabi wajen taron da ya jagoran ta a Israila wanda ya samu halartar ministocin kasashen Larabawa guda 4, Blinken yace zasu ci gaba da lalubo hanyar sasanta bangarorin biyu domin tabbatar da zaman lafiya.
Dangane da wannan matsayi Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami’ar Abuja.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu