Bakonmu a Yau
IMF ya sake kira ga Najeriya kan neman soke tallafin man fetur
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:38
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sake kira ga gwamnatin Najeriya da ta soke tallafin man fetur da kuma farashin canjin kudade a hukumance, tare da daukar matakan rage radadin da hakan zai haifarwa marasa karfi.
Talla
A ranar 24 ga watan Janairun da ya gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta bayyana dage shirinta na cire tallafin man fetur a bana, matakin da IMF ya ce ba zai dore ba.
Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Kasim Kurfi masanin tattalin arziki da ke Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu