Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dan Majalisar Yusuf Adamu Gagdi kan wasikar da ya rubuwata wa shugaba Buhari

Wallafawa ranar:

Ganin Yadda matsalar tsaro dake ci gaba da tabarbarewa a Najeriya, musamman abinda ya kunshi rikicin kabilanci da addini da mayakan Boko Haram da na Yan bindiga dake sace mutane domin karbar diyya da kuma rikicin manoma da makiyaya, ya sa daya daga cikin shugabannin kwamitocin Majalisar wakilan Najeriya Hon Yusuf Adamu Gagdi rubuta budaddiyar wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sojojin Najeriya dake kokarin kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar.
Sojojin Najeriya dake kokarin kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar. Audu Marte AFP
Talla

Dan Majalisar ya koka sosai dangane da yadda zubda jini ya zama ruwan dare da yadda ake hallaka mutane ba tare da kaukautawa ba da kuma yadda gwamnati ta gaza daukar matakan da suka dace.

Bayan rubuta budaddiyar wasikar, mun tambaye shi ko me ya sashi daukar wannan mataki a matsayin sa na dan majalisa wanda suka fito Jam’iyya daya da shugaban kasa. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron hirar da muka yi da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.