Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta shafi mutane fiye da dubu 300 a Nijar

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ke sauka a Jamhuriyar Nijar tun watan Yuni da kuma mummunar ambaliyar ruwa da ya haddasa, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 195, da kuma wasu fiye da dubu da 322,000 da muhallansu.

Wani yanki da ambaliyar ruwa ta mamaye a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.
Wani yanki da ambaliyar ruwa ta mamaye a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar. AFP - BOUREIMA HAMA
Talla

Alkalumman da ke fayyace adadin mutanen da ambaliyar ta rutsa da su a Nijar, ya sanya daminar bana zama mafi  muni a tarihin kasar da a baya tafi fama da karancin saukar ruwan sama.

Bisa kididdigar da aka yi, daga cikin mutane 195 da suka mutu fadin kasar akwai 136 da suka rasa rayukansu sakamakon rushewar gidaje, yayin da wasu 59 suka nutse a ruwa.

Kididdigar ta kara da cewar, mutane 211 sun jikkata.

Yankunan da ambaliyar ruwa ta fi shafa, sun hada da Yamai, da Maradi, da Dosso, da Diffa da kuma Tahoua.

A yankin Difa kadai, gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce sama da mutane dubu 11 ambaliyar ruwa ta shafa, bayan da kogin Komadugu ya yi ambaliya cikin makon da ya gabata.

Fira ministan kasar Uhmudu Mahammadu ya ce gidaje dubu 2 da 138 ne suka rushe, yayin da gonaki da dama suka lalace a yankin na Diffa saboda wannan ambiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.