Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane fiye da 150 a Nijar

Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun mutane 159 suka mutu bayan da aka shafe watanni ruwan sama kamar da bakin kwarya na sauka a sassan kasar.

Yadda ambaliya ta mamaye wani yanki a Jamhuriyar Nijar.
Yadda ambaliya ta mamaye wani yanki a Jamhuriyar Nijar. BOUREIMA HAMA / AFP
Talla

Kwararru dai sun bayyana ambaliyar ruwan bana da aka fuskanta a Nijar a matsayin daya daga cikin mafi muni da aka gani a tarihin kasar.

Kididdigar da gwamnati ta fitar ta nuna cewar mutane 121 suka rasa rayukansu sakamakon rushewar gidajen da ya rutsa da su, yayin da wasu 38 suka mutu sakamakon nutsewa cikin ruwa, tun bayan fara saukar ruwan sama a daminar bana.

Baya ga hasarar rayukan mutanen da aka samu, dubban gine-gine, da suka hada da gidaje da makarantu da cibiyoyin kula da lafiya sun rushe sakamakon ambaliyar da ta biyo bayan saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Akalla mutane dubu 225,539 iftila’in ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jamhuriyar Nijar, yayin da wasu karin 200 suka jikkata.

Yanzu haka dai Nijar na fuskantar matsalar karancin abinci a wasu sassan kasar kamar yadda kwararru suka yi gargadi, tare da jan hankali da cewar fiye da mutane miliyan 4 ke cikin hatsarin fadawa yunwa, kwatankwacin kashi 1 bisa 5 na yawan al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.