Isa ga babban shafi

Masu bincike sun gaza gano dalilin tsare motocin Sojin Faransa a Nijar

Ma’aikatar cikin gida a Jamhuriyar Nijar ta bayyana cewa sakamakon binciken kwararru ya gaza gano musabbabin tarzomar da ta kai ga kisan mutane 3 cikin watan Nuwamban bara lokacin da tawagar Sojin Faransa ke shirin ratsawa ta kasar don shigar da makamai Mali.

Shugaban Jumhuriyar Nijar Bazoum Mohamed yayin wanim taro a Niamey babban birnin Kasar, 13 ga watan Mayu shekarar 2022.
Shugaban Jumhuriyar Nijar Bazoum Mohamed yayin wanim taro a Niamey babban birnin Kasar, 13 ga watan Mayu shekarar 2022. © Presidence du Niger
Talla

Sanarwar da ma’aikatar cikin gidan ta Nijar ta fitar a yau laraba, ta ce bayan dogon binciken hadin gwiwa tsakanin jami’an Jandarma da Sojin Faransa, ba a kai ga gano musabbabin tarzomar ta watan Nuwamba da ta hallaka mutane 3 tare da jikkata wasu da dam aba.

Sanarwar ta ce gwamnatin Nijar da Faransa sun amince da biyan diyyar mutanen da suka rasa rayukansu a tarzomar ko da ya ke sanarwar ba ta fayyace diyyar adadin mutanen da za a bayar ba la’akari da yadda aka samu rarrabuwar kai game da yawan mutanen da suka mutu a hatsaniyar.

Sanarwar ta ce binciken ya gano laifin jami’an tsaron Nijar da ke tare da tawagar makaman wadanda suka gaza daukar matakan da suka kamata wajen kwantar da hankula a lokacin tarzomar, wanda ya tilasta Sojin Faransa daukar matakin kare kansu daga fushin jama’a ta hanyar amfani da bindiga.

Tun da farko tawagar motocin yakin Faransar makare da makamai da ke kan hanyar shigar da makamai Mali sun gamu da tirjiyar jama’a a yankin Kaya na tsakiyar Burkina Faso wadanda suka rika jifarsu dalilin da ya sanya tawagar bi ta yankin Tera da ke yammacin Nijar inda a nan ma aka gamu da tirjiyar jama’a da ya kai ga kisan fararen hula 3 tare da jikkata wasu da dama.

Cikin watan Disamban bara ne shugaban Nijar Mohamed Bazaoum ya yi umarnin gudanar da bincike kan tarzomar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.