Isa ga babban shafi
nijar

Ana tsare wani tsohon minista a Nijar saboda yunkurin juyin mulki

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tasa keyar tsohon ministan cikin gida karkashin mulkin soja na Salou Djibo, kwamishinan 'yan sanda Cissé Ousmane Ibrahim di da akafi sani da "Loulou", zuwa gidan yarin Birni Ngaoure dake kusa da Yamai.

Jami'an 'yan sandan jamhuriyar Nijar
Jami'an 'yan sandan jamhuriyar Nijar © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Wasu daga cikin ‘yan uwansa sun tabbatar wa manema labarai yadda aka gaggauta tura Lolou Kurkuku, Karkashin wani sammaci kan tuhumar da ake masa dangane da yunkurin juyin mulkin a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2021.

Ranar Jumma'a aka tsare Loulou

Da sanyin safiyar Juma’a ne jami’an tsaron farin kaya suka kama shi, inda aka saurare shi, nan take aka mika tsohon Darakta Janar na ‘yan sandan kasar zuwa gaban masu gabatar da kara, sannan aka gabatar da shi ga shugaban alkalan da ke binciken wanda daga baya kuma a rana guda aka ba shi takardar sammacin aikata laifuka, tarer da tura shi gidan yarin farar hula na Birnin Ngaouré mai tazarar kilomita 100 kudu maso gabas da Yamai a yankin Dosso.

Yunkurin juyin mulki

A cewar wasu 'yan uwansa, "Loulou", wanda ya dawo daga aiki a matsayin jakadan Nijar a Chadi da Afirka ta Tsakiya, ana zarginsa da "kawo cikas ga tsaron kasa", a wani bangare na binciken yunkurin juyin mulkin ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2021.

A daren ranar 31 ga watan Maris, 2021, kwanaki kadan gabanin mika mulki tsakanin Issoufou Mahamadou da Bazoum Mohamed, an yi harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasar da ke Yamai. Bayan 'yan sa'o'i kadan, gwamnati ta ba da sanarwar cewa an dakile wani "yunkurin juyin mulki" kuma an kama mutane da yawa yayin da aka fara neman wasu".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.