Isa ga babban shafi
Nijar - Muhalli

Gwamnatin Nijar ta rufe mahakar Zinaren Dan-Isa

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da rufe mahakar Zinare ta Dan-Isa kwata-kwata, bayan da kwamitin da aka kafa da ya kunshi kwararu ya ce,  akwai hatsari sosai wajen ci gaba da aikin hakar ma’adinin.

Yadda ma'aikata suka dukufa wajen aikin hako Zinare a garin Kwandago da ke yankin Dan-Isa a Jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar.
Yadda ma'aikata suka dukufa wajen aikin hako Zinare a garin Kwandago da ke yankin Dan-Isa a Jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar. © RFI Hausa/Salissou Issa
Talla

Matakin ya zo ne duk da cewa, dubban mutane sun yi ta kiraye-kirayen a bude mahakar don ci gaba da neman abincinsu.

Sama da mutane dubu 30 ne dai ke aiki a filin hakar Zinaren da fadinsa ya kai kilomita 5.

Daga Maradi Salisu ya aiko mana rahoto kan halin da ake ciki.

01:37

Rahoto akan rufe wurin hakar Zinare a Dan Isa da ke jamhuriyar Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.