Isa ga babban shafi
Nijar-Gobara

Gobara ta kashe daliban makaranta 26 a jamhuriyar Nijar

Rahotanni daga Jamhuriyyar Nijar sun tabbatar da mutuwar daliban makaranta 26 a wata gobara da ta tashi cikin ajinsu a jihar Maradi da ke yankin kudu maso yammacin kasar.

Wata makaranta da gobara ta kone a birnin Yamai.
Wata makaranta da gobara ta kone a birnin Yamai. AP - Boureima Issoufou
Talla

Magajin garin Maradi Chaibou Aboubacar yayin zantawarsa da manema labarai ya ce zuwa yanzu sun tabbatar da gawarwakin dalibai 26 sai kuma wasu 13 da suka jikkata a gobarar.

Acewar magajin garin, galibin daliban da ibtila’in ya rutsa da su kananan yara ne da shekarun bai haura biyar zuwa 6 ba.

Rahotanni sun ce ajin da lamarin ya faru an yi ginin shi ne da nau’in ciyawar kaba da kuma katako, wanda ya baiwa gobarar damar fantsama cikin sauri.

Jamhuriyyar ta Nijar da ke jerin kasashe mafiya talauci a Duniya na gudanar da gine-ginen azuzuwan makarantu ne a wasu sass ana kasar ta hanyar amfani da katako da kuma kaba yayinda dalibai a wasu lokutan kan zauna a dandanin kasa don daukar darasi.

Magajin garin Maradi Chaibou Aboubacar yayin zantawarsa da manema labarai ya ce zuwa yanzu sun tabbatar da gawarwakin dalibai 26 sai kuma wasu 13 da suka jikkata a gobarar.

Yawaitar samun gobara a makarantun Jamhuriyar Nijar na kokarin zama ruwan dare a baya-bayan nan inda ko a watan Aprilun da ya gabata dalibai 20 suka rasa rayukansu yayin makamanciyar gobarar a Yamai babban birnin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.