Isa ga babban shafi
Nijar - Diffa

Bazoum ya jagoranci maida 'yan gudun hijira gidajensu a Diffa

Yau Alhamis shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed ke gudanar da ziyarar aiki a garin Diffa dake kudu maso gabashin kasar, don ganin yadda aikin mayar da wadanda rikicin Boko Haram ya tilastawa barin garuruwansu ke tafiya.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum yayin ziyarar da ya kai sansanin sojoji dake Bosso, a yankin, zamanin da yake rike da mukamin ministan harkokin cikin gida. 17/6/2016.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum yayin ziyarar da ya kai sansanin sojoji dake Bosso, a yankin, zamanin da yake rike da mukamin ministan harkokin cikin gida. 17/6/2016. © AFP - Issouf Sanogo
Talla

A lokacin wannan ziyara, shugaba Bazoum zai nazarci yanayin tsaro a yankunan da aka fara mayar da fararen hula, wadanda suka fara tserewa daga garuruwa da dama na jihar ta Diffa tun 2015.

Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum wanda aka zaba a watan Fabrairu, a lokacin yakin neman zabensa ya sha alwashin maido da ilahirin ‘yan gudun hijirar da wadanda yaki ya daidaita gidajensu zuwa karshen shekarar 2021.

Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya, a sansanin Asanga dake gaf da garin Diffa a Jamhuriyar Nijar. 16/6/2016.
Wasu 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya, a sansanin Asanga dake gaf da garin Diffa a Jamhuriyar Nijar. 16/6/2016. © ISSOUF SANOGO / AFP

Yanzu haka dai akwai ‘yan gudun hijira akalla dubu 300 da suka tsere wa hare-haren mayakan Boko Haram, daga cikin adadin ‘yan gudun hijirar kuma kimanin dubu 120 sun tsallaka Jamhuriyar ta Nijar ne daga Najeriya.

A kusan karshen watan Yuni gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce mutane kusan dubu 6 sun koma gidajensu dake garin Baroua a yankin Diffa, inda suka kaurace wa tun shekarar 2015 saboda rikicin Boko Haram.

Mutanen kusan dubu 6 kashin farko ne na jerin ‘yan gudun hijirar da gwamnati ke shirin maidawa muhallansu dake a garuruwa da kauyuka akalla 19 a yankin na Diffa mai iyaka da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.