Isa ga babban shafi
Nijar-'Yan gudun hijira

'Yan gudun hijirar Nijar dubu 6 sun koma gidajensu a yankin Diffa

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ce mutane kusan dubu 6 sun koma gidajensu dake garin Baroua a yankin Diffa, inda suka kaurace wa tun shekarar 2015 saboda rikicin Boko Haram.

Wasu 'yan gudun hijirar Niger a yankin  Diffa.
Wasu 'yan gudun hijirar Niger a yankin Diffa. AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA
Talla

Mutanen kusan dubu 6 su ne kashin farko na jerin ‘yan gudun hijirar da gwamnatin Nijar ke shirin maidawa muhallansu dake a garuruwa da kauyuka akalla 19 a yankin na Diffa mai iyaka da Najeriya.

Yanzu haka dai akwai ‘yan gudun hijira akalla dubu 300 da suka tsere wa hare-haren mayakan Boko Haram, daga cikin adadin ‘yan gudun hijirar kuma kimanin dubu 120 sun tsallaka Jamhuriyar ta Nijar ne daga Najeriya.

Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum wanda aka zaba a watan Fabrairu, a lokacin yakin neman zabensa ya sha alwashin maido da ilahirin ‘yan gudun hijirar da wadanda yaki ya daidaita gidajensu zuwa karshen shekarar 2021.

Yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira dubu 60 a cikin Nijar da suka tsere wa rikicin ‘yan ta’adda daga Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.