Isa ga babban shafi
Nijar - Chad

Sabon Shugaban Chadi na ziyara a Jamhuriyar Nijar

Sabon shugaban kasar Chadi Janar Mahamat Idris Deby yak ai ziyarar farko zuwa wata kasar waje zuwa Jamhuriyar Nijar, kasar da suke hadin kai wajen yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

Sabon shugaban kasar Chadi Janar Mahamat Idris Deby yayin gaisawa da shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed bayan isa birnin Yamai.
Sabon shugaban kasar Chadi Janar Mahamat Idris Deby yayin gaisawa da shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed bayan isa birnin Yamai. © Niger Presidency
Talla

Yayin ziyarar birnin Yammai, shugaba Deby ya tattauna da takwaran sa kuma zababben shugaban kasa Bazoum Mohammed kan batutuwan hadin kai da suka shafi kasashen biyu.

Rahotanni sun ce ana saran Janar Deby ya ziyarci dakarun kasar sa da ke aiki a kudancin Nijar domin yaki da yan ta’adda.

Wani jami’in shugaba Bazoum Mohammed ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar kasar Chadi na da dakaru 1,200 a kudancin Nijar dake karkashin rundunar G5 Sahel wadanda aka aje a Tera, domin bunkasa tsaron yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.