Isa ga babban shafi
Chadi-Nijar

Jamhuriyar Nijar ta karrama Idris Deby da lambar yabo mafi girma

Jamhuriyar Nijar ta bai wa shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno lambar yabo mafi girma ta kasar, sakamakon rawar da yake takawa don samar da zaman lafiya da kuma tsaro a yankin Sahel.

Shugaban Chadi Idriss Deby Itno
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno REUTERS/Carlo Allegri
Talla

An bai wa shugaba Idris Deby wannan kyauta ce a ziyarar da ya kai a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar a wannan labara, don ganawa da sojojinsa da ke kan hanyar zuwa fagen daga a kusurwar kasashen Nijar, Burkina Faso da kuma Mali don fada da ayyukan ta’addanci.

Idris Deby na wannan ziyara ce domin karfafawa dakarunsa guiwa, inda takwaransa Issoufou Mahamadou ya sanar da ba shi lambar yabo mafi girma ta kasar mai suna Grand-Croix de l’Ordre National du Niger, saboda a cewar Issoufou Mahamadou, ko baya ga tabbatar da tsaro, takwaran nashi na Chadi ya bayar da gudunmuwa wajen samar da ci gaba a yankin.

Hakazalika an bai wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari irin wannan lamba ta yabo, duk sakamakon kokarinsu wajen samar da zaman lafiya a yankin.

Da farko dai an tsara bai wa shugabannin biyu wadannan lambobi na yabo ne a lokacin bikin zagayowar ranar jamhuriyar wato 18 a watan disamba amma aka dage saboda wasu dalilai.

Idris Deby ya ziyarci dakarun kasar ta Chadi ne da ke jibge a wajen birnin Niamey, tare da rakiyar takwaransa Issoufou Mahamadou, da kuma babban kwamandan rundunar hadin-guiwa ta G5 Sahel wato janar Oumarou Natama Gazama.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.