'Yan bindiga sun tarwatsa 'yan gudun hijira a Nijar
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa dubban mutane ne suka tsere daga sansanin ‘yan gudun hijira da ke Intikane a cikin jihar Tawa gab da iyakar kasar da Mali, bayan da ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe mutane a kalla 3 a ranar Lahadin da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Ofishin Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya da ke Nijar ya ce, yanzu mutane dubu uku da suka tsere sun samu mafaka a garin Tlemces mai tazarar kilomita 27 daga sansaninsu na farko.
A kalla dai ‘yan asalin kasar Mali dubu 20 ne ke rayuwa a sansanin da aka kai wa harin, tare da wasu dubbai ‘yan Nijar da suka guje wa tashe-taashen hankulan da ake fama da su
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu