Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnan Borno ya soma shirin maida 'yan gudun hijira dubu 120 gida

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya soma tattaunawa da hukumomin Jamhuriyar Nijar, kan shirin karbar ‘yan gudun hijira dubu 120 da rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa zuwa kasar.

Gwaman Jihar Borno Farfesa Baba Gana Umara Zulum lokacin da ya sauka a jamhuriyar Nijar domin ziyarar 'yan gudun hijirar jiharsa.
Gwaman Jihar Borno Farfesa Baba Gana Umara Zulum lokacin da ya sauka a jamhuriyar Nijar domin ziyarar 'yan gudun hijirar jiharsa. Borno Government
Talla

Dubban ‘yan gudun hijira ne dai yanzu haka ke samun mafaka a kasar ta Nijar, Chadi da kuma Kamaru a dalilin rikicin na Boko Haram da ya shafe sama da shekaru 10.

Mafi akasarin wadanda suka tsere da jihar Borno da wasu sassan arewa maso gabashin Najeriya dai na zaune ne a sansanonin ‘yan gudun hijira dake yankin jihar Diffa a Jamhuriyar ta Nijar, inda a ranar asabar 15 ga watan Fabarairu, gwamnan na Borno Farfesa Babagana Zulum ya ziyarta.

Rahotanni sun ce kafin ziyartar Nijar, gwamnan Zulum ya gana da jami’an ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya da na hukumomin kula da ‘yan gudun hijira kan shirin karbar ‘yan jihar Borno dake gudun hijira a sansanonin da aka kafa musu a wasu sassan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.