Isa ga babban shafi
Nijar

An daure Ousmane saboda tinzira sojojin Nijar

Wata kotu a Jamhuriyar Nijar ta yanke wa wani mai rajin kare hakkin bil Adama Abdoulmumin Ousmane hukuncin daurin wata shida a gidan yari bayan ta tuhume shi akan tinzira sojojin kasar dangane da karban mulki.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Wanda ake zargin ya yi sharhi ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce shugaban kasar Mahamadou Issofou na kame-kame kawai wajen yaki da kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da tayar da kayar baya a kasar.

Ousmane ya kara da cewa, shi a ra’ayinsa zai so sojoji su karbe ikon kasar don murkushe 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Sai dai bisa dukkan alamu kalaman na Ousmane bai yi wa 'yan kungiyar farar hula dadi, inda suka bayyana cewa, ya kamata duk wani mai rajin kare hakkin dan Adam ya san irin furucin da zai rika furta wa ko kuma yada wa a bainal jama'a kamar yadda Dauda Tankama ya shaida wa RFI hausa, daya daga cikin shugabannin kungiyar a Nijar.

00:49

Dauda Tankama kan daure Ousmane na Nijar

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.