Isa ga babban shafi

Najeriya ta yi iƙirarin kuɓutar da mutane dubu 1 daga hannun 'yan ta'adda

Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, yace gwamnatin tarayyar kasar a baya-bayan nan ta kuɓutar da mutane sama da dubu 1 daga hannun 'yan ta'adda ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. 8/05/23
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. 8/05/23 AP - Ben Curtis
Talla

Ribadu, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi Malamai da Dalibai 22 na jami’ar Gusau da ke jihar Zamfara, da aka kubutar da su daga hannun 'yan bindiga a ranar Lahadi.

Idan ba’a manta ba tun a ranar 22 ga watan Satumbar 2023 ne ‘Yan bindiga suka shiga jami’ar tare da yin awon gaba da sama Dalibai da Malamai 30.

A nasa jawabin shima da ya kasance a Jami’ar yayin karbar Dalibai da Malaman, mataimakin gwamnan jihar Zamfara Mani Mummuni, ya jajantawa iyalai da kuma hukumar makarantar bisa abinda ya faru.

Mataimakin gwamnan ya kuma bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kubutar da sauran Daliban da aka sace a wasu makarantun kasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Yazid Abubakar ya fitar, ya badaa tabbacin cewa rundunar zata ci gaba da iya bakin kokarinta wajen ganin an kubutar da sauran daliban da ke hannun masu garkuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.