Isa ga babban shafi

Bikin Sallah: Za mu murkushe duk wata barazanar tsaro a jihar Kano-'Yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a tarayyar Najeriya ta ce ta gano wasu batagari da ke kokarin tayar da tarzoma a lokacin bukukuwan Sallah, tana mai cewa ba zata saurarawa duk wanda ya yi yunkurin tayar da hankulan al'umma.

Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya.
Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya. AFP
Talla

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da malaman addinin Muslunci da kuma wakilai daga masarautu biyar na Kano a jiya Litinin.

Yayin ganawar ta jiya Kwamishinan ya tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda za su yi aiki ka’in da na’in domin ganin sun kawar da duk wata barazana da ka iya haifar da yamutsi kafin da lokacin da kuma bayan bukukuwan sallah.

Ya kuma bayyana Kano a matsayin jiha daya tilo da babu wata barazanar tsaro ta’yan bindiga ko masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, lamarin daya alakanta ta da irin namijin kokarin da jami’an tsaro ke yi.

Kazalika Kwamishinan yace sashen leken asiri da binciken kwakwaf na rundunar ya gano wasu ‘yan siyasar da ko dai ba su gamsu da yadda ake jagorancin jihar ba ko kuma ba’a basu mukamai ba, suna nan sun dukufa wajen haifar da hargitsi a tsakanin al’umma.

Saboda haka rundunar ta bukaci al’umma da su kasance masu da’a da kaunar juna, domin wanzuwar zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.