Isa ga babban shafi

Hukumar yakar rashawa ta Kano ta sake gurfanar da Ganduje

Hukumar yakar rashawa da kuma karbar korafe korafe-korafe a Kano da ke tarayyar Najeriya, ta sanar da wasu sabbin tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa da kuma almundahana kan tsohon Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje © Daily Post
Talla

A cewar shugaban hukumar, Muhuyi Magaji, bincike ya gano yadda aka karkatar da naira biliyan 51.3 daga kudaden kananan hukumomi zuwa wasu asusun ajiya a zamanin Ganduje.

Da yake magana a wani gidan talibijin da ke kasar, shugaban hukumar, Muhuyi Magaji ya yi zargin cewa gwamnatin Ganduje na cire Naira biliyan 1 duk wata daga asusun gwamnati kafin wa’adinsa ya kare a watan Mayun 2023, da sunan gyaran tituna, amma sai aka karkatar da su zuwa ga masu gudanar da harkokin canji na Bureau de Change.

Ya kuma bayar da misali da wata shari’a da ta shafi Naira biliyan 4 da aka tura wa wani kamfanin noma daga asusun ajiya na gwamnatin Kano.

“Abin da ke faruwa a yanzu shi ne, kamar yadda nake magana da ku, muna kan bincike kan wata badakala da ta kai Naira biliyan 51.3 na kudaden kananan hukumomi da aka dauko daga asusun gwamnati sannan aka aika zuwa asusun wasu daidaikun mutane, kuma tuni muka gano ko su wanenen,” in ji Muhuyi.

Gwamnatin jihar ta ce za ta gurfanar da Ganduje tare da matarsa da dansa a gaban kuliya bisa zargin karkatar da kudade da sunan yiwa jihar aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.