Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Jami'an EFCC sun kame matar Gwamnan Kano Hafsat Ganduje

Rahotanni daga jihar Kano a Tarayyar Najeriya na cewa jami'an hukumar EFCC sun kame mai dakin gwamnan jihar Hajiya Hafsat Umar Ganduje bayan da ta ki amsa gayyatar da hukumar ta yi mata dangane da badakalar wani fili tsakaninta da danta.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase
Talla

Kamen na zuwa makwanni bayan wa'adin da hukumar ta EFCC ta dibar mata don bayyana gabanta game da takaddamar wadda danta Abdul'aziz Ganduje ya shigar da korafi gaban hukumar don nemar masa hakkinsa.

Tun a ranar 23 ga watan Satumba da ya gabata, hukumar ta EFCC ta bukaci Hajiya Hafsat ta bayyana gabanta amma kuma matar Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje ta ki mutunta gayyatar, ko da ya ke wata makusanciyarta ta shaidawa manema labarai cewa a lokacin mai dakin gwamnan na kasar Birtaniya.

Wasu bayanai daga gidan gwamnatin jihar ta Kano na cewa tun a yammacin jiya litinin jami'an hukumar suka kame Hajiya Hafsat Ganduje, sai dai babu cikakken bayani kan ko ta dawo gida ko kuma tana ci gaba da fuskantar dauri a hukumar gabanin fara sauraron bahasi kan korafin.

Tun farko Abdul'aziz Ganduje ne ya fara kaiwa EFCC batun don ganin hukumar ta shiga tsakani don kwatar masa hakkinsa da ya ce mahaifiyartasa na kokarin yi masa sama da fadi akai.

Bayanai sun ce almundahana da rashawa sun dabaibaye lamarin filin tsakanin Hafsa Ganduje da dan nata Abdul'aziz.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Iyalan gwamnan na Kano ke tsintar kansu a lamurra masu alaka da cin hanci rashawa ko kuma almundahana ba, la'akari da cewa shi kansa Gwamnan akwai zarge-zarge da suka dabaibaye tsarin tafiyar da mulkinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.