Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun farmaki tawagar motar Gwamnan Kano Ganduje

'Yan Bindiga a Najeriya sun kai hari kan tawagar motocin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje lokacin da ya ke barin Zamfara domin komawa gida abinda ya yi sanadiyar jikkata jami’an 'yan sanda guda 3 da ke rakiyar sa.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. africatodaynewsonline
Talla

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar Yan bindigar sun bude wuta akan jerin motocin Gwamnan ne bayan kammala taron Jam’iyyar APC da akayi a birnin Gusau inda Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP.

Majiyar fadar gwamnatin Kano tace Gwamna Ganduje baya cikin motar sa lokacin da Yan bindigar suka bude wuta akan tawagar motocin.

Rahotanni sun ce Ganduje yabi tawagar Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar komawa gida, yayin da tawagar motocin sa suka bi shi.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da Yan bindigar suka harbe dan majalisar jihar Zamfara Mohammed Ali Ahmed dake wakiltar Shinkafi akan hanyar sa ta zuwa Funtua daga Gusau bayan kamala taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.