Isa ga babban shafi

Bai kamata Najeriya ta kyale kamfanin Shell ba - Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International da sauran kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da yarjejeniyar ta da kamfanin Shell musamman game da sayar da kadarorin kamfanin a matsayin wata hanya ta biya diyya ga al’ummonin yankunan da aka gurbatawa muhalli.

Kamfanin dai ya jima yana kai ruwa rana da mazauna kauyuka da suke fama da gurbacewar muhalli, saboda yanayin ayyukansa, musamman a niger-Delta.
Kamfanin dai ya jima yana kai ruwa rana da mazauna kauyuka da suke fama da gurbacewar muhalli, saboda yanayin ayyukansa, musamman a niger-Delta. © Shell
Talla

Al’ummomin yankunan da suka dogara da noma da kamun kifi a yankin Neja-Delta, wato cibiyar samar da danyen mai a Najeriya, sun shafe shekaru suna kai ruwa rana a gaban shari’a kan barnar da malalar mai ke haifar musu.

Kamfanin Shell ya amince ya sayar da kadarorinsa da ke gabar tekun kasar ga wani kamfani mai zaman kansa a Najeriya kan kudi dala biliyan 2.4 yayin da ya koma harkokin kasuwancisa a cikin teku.

A wata budaddiyar wasika da kungiyoyin suka fitar a ranar Litinin, Amnesty da sauran kungiyoyin kare hakkin dan adam a Najeriya da na kasa da kasa sun yi kira ga hukumar da ke kula da harkokin mai a Najeriya da ta yi watsi da batun gwanjon kadarorin Shell ga kamfanin Renaissance African Energy.

Wasikar ta ci gaba da cewa, bai kamata a ba da izinin sayar da kadarorin Shell ba, sai dai idan an tuntubi al’ummomin yankin da abin ya shafa, wadanda ke fama da gurbacewar muhalli musamman game da yadda za a samar da kudaden da za a kashe wajen tsaftace muhallan su.

Har yanzu dai kamfanin na Shell bai ce uffa kan wannan batu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.