Isa ga babban shafi
BOKO HARAM

Yau aka cika shekaru 10 da sace daliban makarantar sakandaren Chibok

Najeriya – Yau aka cika shekaru 10 cur da sace daliban makarantar sakandaren Chibok mata 276 da mayakan boko haram suka yi a Jihar Barno, matsalar da ta gamu da fushin jama’a a ciki da wajen Najeriya.

Wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram a shekarar 2016, yayin da suke ganawa da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, a Abuja.
Wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram a shekarar 2016, yayin da suke ganawa da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, a Abuja. AP - Sunday Aghaeze
Talla

Daliban mata masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18 na makarantar ta gwamnati ne a lokacin domin zana jarabawa, amma mayakan dauke da makami suka musu tsinke dauke da muggan makamai, inda suka sanya su cikin motoci suka kuma gudu da su.

Wannan satar ta janyo hankalin kasashen duniya ciki harda irinsu Amurka da Birtaniya da Faransa da ma Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Turai, wadanda duk suka yi alkawarin taimakawa Najeriya kubutar da daliban da kuma ganin an hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata wannan laifi.

 Hauwa Joseph da Mary Dauda dauke da yaran su bayan sun kubuta daga hannun mayakan boko haram
Hauwa Joseph da Mary Dauda dauke da yaran su bayan sun kubuta daga hannun mayakan boko haram AFP - AUDU MARTE

Akalla dalibai 50 suka gudu daga cikin wadanda aka sace, yayin da gwamnati ta kubutar da wasu ta hannun kungiyar agaji ta Red Cross, kana wasu kuma har zuwa yau babu wanda ya ji duriyar su.

Wadannan mayaka sun auri wasu daga cikin daliban, inda suka ki sakin su da kuma hana su komawa karatu, yayin da aka ga wasu daga cikin su kuma dauke da yaran da suka haifa lokacin da suka dawo cikin jama’a.

Kungiyar masu fafutukar kubutar da daliban Chibok ta 'Bring Back Our Girls'
Kungiyar masu fafutukar kubutar da daliban Chibok ta 'Bring Back Our Girls' 路透社

Satar wadannan dalibai ta bude kofar satar wasu dalibai daban daban a makarantun dake yankin arewacin kasar har sama da makarantu 10, yayin da ‘yan bindiga suka mayar da matsalar hanyar neman kudi.

Ana saran gudanar da bukukuwa a Chibok da Abuja da kuma Lagos domin nuna alhini dangane da wannan iftila’in da ta shafi wadannan dalibai shekaru 10 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.