Isa ga babban shafi
SATAR DALIBAI

Bayan daliban Chibok, sau 10 aka kai hari wasu makarantu domin kwashe dalibai

Najeriya – Bayan sace dalibai mata daga sakandaren Chibok da mayakan boko haram suka yi a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014, an samu wasu sace sacen dalibai da dama da 'yan ta'adda suka yi a garuruwa daban daban a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Wasu daga cikin daliban Chibok da suka kubuta daga hannun mayakan boko haram
Wasu daga cikin daliban Chibok da suka kubuta daga hannun mayakan boko haram AP - Sunday Alamba
Talla

Daga cikin wadannan sace sacen dalibai da mayakn boko haram da kuma 'yan bindigar ke yi domin karbar kudi, da labarin su ya shahara, akwai jerin wadannan sace sacen kamar haka:

A ranar 25 ga watan Fabarairun shekarar 2018, mayakan boko haram sun kai hari makarantar sakandaren mata ta Dapchi dake jihar Yobe, inda suka kwashe dalibai 110.

Daliban sakandaren Dapchi da aka sace
Daliban sakandaren Dapchi da aka sace AFP/File

A ranar 6 ga watan Mayun shekarar 2019, 'yan bindiga sun sace dalibai 8 da malamai 2 a kwalejin Engravers dake jihar Kaduna.

A ranar 11 ga watan Disambar shekarar 2020, dalibai sama da 300 'yan bindiga suka sace daga makarantar sakandaren Kankara dake jihar Katsina.

A ranar 17 ga watan Fabarairun shekarar 2021, dalibai 42 'yan bindiga suka sace a kwalejin aikin gona dake Bakura a jihar Zamfara.

Tsohon kwamandan rundunar yaki da boko haram dake Maiduguri, Manjo Janar Nicolas Rojas, dauke da daya daga cikin daliban Dapchi da ta galabaita bayan kubutar da su
Tsohon kwamandan rundunar yaki da boko haram dake Maiduguri, Manjo Janar Nicolas Rojas, dauke da daya daga cikin daliban Dapchi da ta galabaita bayan kubutar da su REUTERS/Afolabi

A ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2021, dalibai 30 'yan bindiga suka sace a kwalejin aikin gona dake Kaduna.

A ranar 20 ga watan Afrilun shekarar 2021, dalibai 20 aka sace a jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna.

A ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2021, dalibai 150 'yan bindiga suka sace a makarantar Islamiyar Rafi dake jihar Neja.

A ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2021, dalibai akalla 70 da malamai guda 2 'yan bindiga suka sace a kwalejin gwamnatin tarayyar Najeriya dake Yauri a jihar Kebbi.

A ranar 5 ga watan Yuli na shekarar 2021, dalibai sama da 100 'yan bindiga suka sace a makarantar sakandaren Bethel dake Jihar Kaduna.

A ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2024, dalibai kusan 300 'yan bindigar suka sace a kwalejin gwamnatin tarayya dake Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.