Isa ga babban shafi

Shekaru 10 bayan sace 'yan matan Chibok 276, sace-sacen ya karu a Najeriya

Cikin daren Litinin 14 ga watan Afrilu zuwa Talata 15 ga watan Afrilu, 2014, mayakan Boko Haram sun yi garkuwa da ‘yan matan sakandare 276 daga makarantarsu da ke arewa maso gabashin Najeriya.Rikicin na Chibok ya haifar da ce-ce-ku-ce a duniya amma bayan shekaru goma, da yawansu ba a gansu ba, kuma sace-sacen da ake yi a makarantu ya karu a wannan kasa.

Zanen matan Chibok 108 da Boko Haram ta yi garkuwa da su, da aka baje kolinsu a Legas, a cewar mai zane Prune Nourry.
Zanen matan Chibok 108 da Boko Haram ta yi garkuwa da su, da aka baje kolinsu a Legas, a cewar mai zane Prune Nourry. REUTERS - SEUN SANNI
Talla

Wannan sace-sacen da kungiyar Boko Haram ke yi ya haifar da fargaba a Najeriya da ma fiye da haka.

Isa Sanusi, wanda a yanzu daraktan kungiyar Amnesty International a Najeriya, ya na cewa “ a wani bincike da suka gudanar jim kadan bayan faruwar wannan bala’i.

Wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram a shekarar 2016, yayin da suke ganawa da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, a Abuja.
Wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram a shekarar 2016, yayin da suke ganawa da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, a Abuja. AP - Sunday Aghaeze

Ya bayyana cewa an sanar da jami’an tsaro cewa za a iya kai hari, ya ci gaba da cewa, sai dai babu wanda ya yi wani abu. An yi mummunar tabarbarewar tsaro. »

Bayan kai harin, ‘yan matan sakandare 57 sun yi nasarar tserewa ta hanyar tsalle daga cikin motocin da ake dauke da su.

Kungiyar Boko Haram ta rabu gida biyu kuma shugabanta na lokaci Abubakar Shekau, ya kashe kansa a watan Mayun 2021, bayan wani farmaki da mayakan kungiyar IS da ke yammacin Afirka (Iswap) suka kai a dajin Sambisa.

Karin 'yan matan sakandaren Chibok guda biyu da sojojin Najeriya suka gano bayan tserewa daga hannun mayakan Boko Haram.
Karin 'yan matan sakandaren Chibok guda biyu da sojojin Najeriya suka gano bayan tserewa daga hannun mayakan Boko Haram. © RFI Hausa / Bilyaminu Yusuf

Yayin da wasu daga cikin ‘yan matan da aka sako aka samu damar kula da su a cibiyoyin ilimi, wasu kuma ba su koma karatu ba. Yawancin kuma ba su amfana da tallafin da ya dace ba, duk da raunin da aka yi na tsare su.

A garin Yola inda RFI ta gana da su, Amina da Jummai, wadanda suka tsira daga Chibok, sun yi magana kan karya alkawuran da gwamnatin Najeriya ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.