Isa ga babban shafi
MATSALAR TSARO

Mayakan boko haram sama da dubu 200 suka aje makaman su a Barno - Gwamnati

Najeriya – Gwamnatin Jihar Barno dake Najeriya, tace akalla mayakan boko haram sama da dubu 200 suka aje makaman su domin rungumar shirin sasantawar da take jagoranci, yayin da wasu da dama kuma ke ci gaba da fitowa daga daji suna karbar shirin.

Gwamnan jihar Borno a Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum.
Gwamnan jihar Borno a Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum. © Borno state government
Talla

Mai magana da yawun gwamnan jihar Baba Sheikh ya shaidawa RFI Hausa wannan nasarar da suka samu a ziyarar aikin da ya kai birnin Lagos.

Sheikh yace kafin kaddamar da shirin sanda gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya gayyaci duk masu ruwa da tsaki a Barno domin tattauna yadda za'a kaddamar da shi domin bai wa matasan damar dawowa cikin al'umma, yayin da a bangare guda sojoji kuma ke can suna fafatawa da wadanda suka ki amincewa da shirin.

Jami'in yace bayan samun amincewar shugabannin al'ummomin jihar, gwamnati ta kaddamar da shirin na kwance damara da sauya tunanin mayakan da kuma sake mayar da su cikin al'umma, wanda yace tuni ya samu karbuwa da kuma goyan bayan Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres wanda ya ziyarci jihar.

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin gaisawa da Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum tare da tawagarsa, ranar 3 ga Mayu, 2022.
Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin gaisawa da Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum tare da tawagarsa, ranar 3 ga Mayu, 2022. © REUTERS/Afolabi Sotunde

Sheikh yace a karkashin wannan shirin, gwamnatin jihar ta samar da wuri inda take karbar tubabbun da kuma horar da su wajen sauya musu tunani sakamakon yadda gurbata musu tunani a daji, kuma daga karshe a kan mayar da su cikin al'umma da kuma basu abinda za suyi sana'a bayan an horar da su.

Jami'in yace ko a 'yan kwanakin da suka gabata, sanda jakadun kasashen yammacin duniya 14 da na Japan suka ziyarci Maiduguri domin bayyana goyan bayan su ga shirin da kuma duba hanyar yadda zasu taimakawa ma ta.

Sheikh ya kuma bayyana cewar, sabanin yadda wasu jama'a ke tunani, ya zuwa wannan lokaci babu wata karamar hukuma a jihar dake karkashin wadannan masu tada kayar baya, saboda yadda sojoji ke gudanar da aikin su da kuma yadda shirin sasancin ke samun galaba.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya ziyarci Auno bayan harin Boko Haram da ya kashe kimanin mutane 30
Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya ziyarci Auno bayan harin Boko Haram da ya kashe kimanin mutane 30 TheCable

Ya kara da cewa, wannan nasarar ce ta bada damar mayar da dubban 'yan gudun hijira zuwa garuruwan su, bayan sake gina musu gidaje da cibiyoyin kula da lafiya da kuma kayan more rayuwa, bayan sojoji sun tabbatar da cewar tsaro ya inganta.

Sheikh yace ya zuwa yanzu da dama daga cikin masu sana'ar noma sun koma gonakin su domin ci gaba da sana'ar su, kamar yadda 'yan kasuwa suka koma kasuwanni, yayin da aka sake bude makarantun da aka gyara tare da cibiyoyin kula da lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.