Isa ga babban shafi

Yan wasan Najeriya mata sun fi takwarorinsu maza a fagen wasanni

Tawagar 'yan wasan Najeriya 358 ta samu gagarumar nasara a gasar wasannin Afrika karo na 13 da aka kammala a Ghana. Yan wasan Najeria mata musamman sun nuna wasannin da ba za a iya mantawa da su ba ,kamar yadda Omolara Ogunmakinju ta yi nasara a wasan tsere da kuma nasarar da kungiyar kokawa ta yi na lashe lambobin zinare. Gabaɗaya, waɗannan ƴan wasan sun ci gaba da nuna yadda ƴan wasan Najeriya mata suka zarce takwarorinsu maza a wasannin duniya.

'Yan kungiyar kwallon kafa ta matan Nigeria, Super Falcons suna atisaye
'Yan kungiyar kwallon kafa ta matan Nigeria, Super Falcons suna atisaye AFP PHOTO / UWE ANSPACH
Talla

Rahotanni bayan wannan gasa na nuna cewa :duk da cewa kasa da rabin ‘yan Najeriya mata ne, amma 35 daga cikin lambobin zinare 47 da ‘yan wasan Najeriya suka samu mata ne suka samu.

Jimillar lambobin yabo 71 na ‘yan wasan Najeriya mata sun samu kashi 58.67 cikin 100 na adadin da kasar ta samu a wasannin.

Omolara Ogunmakinju, wacce ta mayar da azurfa ta zama zinari a tseren mita 4x400, da kuma yadda matan Najeriya suka mamaye tabarmar kokawa ya misalta yadda suka kasance a gasar.

'Yan kokawa mata shida sun yi rajistar shiga gasar - Odunayo Adekuoroye, Blessing Oborududu, Mercy Genesis, Hannah Reuben, Tolulope Ogunsanya, da Esther Kolawole  wandada suka samu lambobin zinare. Sarauniyar tseren Najeriya, Oluwatobiloba Amusan, wacce ta lashe zinare karo na uku a jere a gasar, ita ma ta tabbatar da matsayinta a matsayin ‘yar wasa ta duniya.

Wasannin Olympics a Faransa
Wasannin Olympics a Faransa AFP - LUDOVIC MARIN

 

Tashin Wasannin Mata A Najeriya

Namiji mai damben boksin Nojim Maiyegun ya lashe lambar yabo ta Olympics ta farko a Najeriya a wasannin Tokyo na 1964. Kambun farko da matan Najeriya suka samu shi ne a gasar Barcelona a shekarar 1992, inda ‘yan wasa hudu na Mary Onyali, Beatrice Utondu, Faith Idehen, da Christy Opara-Thompson suka samu tagulla a tseren gudun mita 4×100 na mata. Ko da yake, wata mace mai suna Chioma Ajunwa, ta samu lambar zinare ta farko a Najeriya lokacin da ta tsallake zuwa mita 7.12 a gasar 1996 a Los Angeles.

 

Gasar Olympics na Rasha  a shekara ta 1980
Gasar Olympics na Rasha a shekara ta 1980 © AP

 

Daga gasar Olympics ta 2000, 'yan wasan mata sun tashi. Daga cikin lambobin yabo 13 da Najeriya ta samu a gasar Olympics, mata sun samu bakwai. Biyu daga cikin lambobin yabo shida da abokan aikinsu maza suka samu sun zo ne a fagen kwallon kafa (2008 da 2016).

Kwatancen ya fi girma a wasannin kasashe masu amfani da harshen ingilishi ko Commonwealth. Najeriya ta samu lambobin yabo 149 tun daga shekarar 2002, kuma a cikin wadannan bugu shida, mata sun samu lambobin yabo 88. Wannan baya zana hoton cikakken rinjaye har sai an lura da sashin lambar zinare. Matan sun samu lambobin zinare 35 daga cikin 48 da kungiyar Nigeria ta dauko. A bugu na karshe da aka yi a birnin Birmingham na kasar Ingila, matan sun lashe dukkan lambobin zinare 11 da Najeriya ta samu.

 

Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafar Najeriya super eagle yayin wasan da aka fafata tsakanin Ghana da Najeriya a Abuja
Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafar Najeriya super eagle yayin wasan da aka fafata tsakanin Ghana da Najeriya a Abuja © NFF

 

A gasar Afrika ta 2024 a wasan daga nauyi, Najeriya ta lashe lambobin zinare shida. Biyar daga cikin wadannan mata ne - Jacinta Umunnakwe mai nauyin kilo 81, Blessing Oraekwe (70kg), Cynthia Ogunsemilore (60kg), Patricia Mbata (75kg), da Joy Nene Ojo (57kg).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.