Isa ga babban shafi

Mutane dubu 289 sun bar muhallansu sakamakon ayyukan ta'ddanci-Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke Arewancin Najeriya ta ce hare-haren ‘yan bindiga ya tilastawa mutane dubu 289 da 375 daga kauyuka 551 na kananan hukumomin jihar 12 barin matsugunansu.

Jihar Kaduna tana fama da hare-haren 'yan bindiga
Jihar Kaduna tana fama da hare-haren 'yan bindiga © dailytrust
Talla

Babban daraktan hukumar kai daukin gaggawa ta jihar Kaduna Usman Mazadu ke sanar wannan alkaluma yayin da yake kaddamar da aikin rarraba kayakin tallfin abinci a Maraban Kajuru ranar Laraba.

A cewar Mazadu, a karamar hukumar Chikun kadai mutane dubu 26 da 345 daga kauyuka 134 ne suka tsere daga matsugunansu saboda tsanantar hare-haren ‘yan bindigar.

Kazalika mutane dubu 70 da 893 daga kauyuka 84 na karamar hukumar Birnin Gwari suma sun tsere daga matsugunnan su sakamakon ayyukan 'yan bindigar.

Yace gwamnatin tarayya da ta Jihar Kaduna suna iya bakin kokarinsu don ganin zaman lafiya ya wanzu a yankunan da ma kasar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.