Isa ga babban shafi

El Rufai ya jefa jihar Kaduna cikin tsaka mai wuya - Sanata Sani

Najeriya – Tsohon ‘dan majalisar dattawan jihar Kaduna dake Najeriya, Sanata Shehu Sani yace dubu ne ta cika wa tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El Rufai dangane da basusukan da ya laftawa jihar lokacin da yake rike da mukamin gwamna.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai. © Daily Trust
Talla

Sanatan yace ya sha zagi iri iri lokacin da yaki amincewa da shirin ciwo bashin daga Bankin duniya, yayin da aka gabatar domin mahawara a majalisar dattawa.

Gwamnan Kaduna Uba Sani ne ya bayyana irin halin kuncin da jihar ke ciki sakamakon bashin da yace ya kai dala miliyan 587 da wasu naira biliyan 85 da kuma kudaden kwangila naira biliyan 115.

Gwamnan yace wadannan basussukan da ake cirewa a kudaden da ake warewa jihar daga gwamnatin tarayya kowanne wata, na hana su gudanar da ayyuka da kuma biyan albashin ma’aikata.

Tsohon Sanatan yace da El Rufai ya saurari shawarar sa a wancan lokacin watakila da jihar bata samu kanta a irin wannan halin tsaka mai wuya ba, wadanda gudanar da mulki ke neman gagara.

Sani ya shaidawa jaridar Aminiya cewar, lokacin da Kaduna ta karbi bashin dala miliyan 350 daga Bankin duniyar, ana canja dala ne a kan naira 400, yanzu kuma ga shi dalar ta zarce naira dubu guda, abinda ke nuna yadda bashin ya ribanya.

A shekarar 2018, sanatocin Jihar Kaduna da suka hada da Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi da kuma Danjuma Laah sun ki amincewa da shirin karbo rancen da aka gabatar a majalisa, matakin da ya gamu da suka sosai daga gwamnatin jihar Kaduna, yayin da El Rufai ya zarge su a matsayin wadanda basa son ci gaban jihar.

Daga bisani Sani da Hunkuyi duk sun rasa kujerun su a majalisar dattawan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.