Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta kara kudin wutar lantarki ga 'yan kasar

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta amince da karin kudin wutar lantarki da 'yan kasar ke biya karkashin rukunin A na kwastamomi wanda ke fara aiki daga wannan Larabar.

Les pénuries d'électricité en Chine affectent désormais les foyers.
Les pénuries d'électricité en Chine affectent désormais les foyers. AP - Andy Wong
Talla

Mataimakin shugaban hukumar, Musliu Oseni ya shaida wa taron manema labarai a birnin Abuja cewa, a karshin wannan sabon karin, 'yan kasar za su rika biyan naira 225 na kilowatt cikin sa'a guda, sabanin naira 66 da suka saba biya kafin sabon tsarin.

Kwastamomin da ke karkashin rukunin A, na shan wutar lantarki na tsawon sa'o'i 20  a kullum.

Oseni ya ce, wadannan kwastamomin na wakiltar kashi 15 na mutanen da ke biyan kudi don shan wutar lantarkin a Najeriya.

Babban jami'in na Hukumar Kula da Wutar Lantarkin ya kara da cewa, sun kuma mayar da wasu kwastamominsu zuwa rukunin B daga rukunin A na masu shan wutar lantarkin saboda rashin ba su wutar na tsawon sa'o'i 20 a kowacce rana.

Sai dai jami'n ya ce, sabon tsarin karin kudin ba zai shafi sauran bayin Allah da ke shan wutar lantarkin a karkashin sauran rukunnan da ake da su a kasar ba.

Ƙarin farashin gas ya sanya fargabar yiwuwar kara kuɗin lantarki a Najeriya

Da ma matakin hukumar da ke kula da hada-hadar albarkatun man fetur na karin farashin gas ya sanya fargabar yiwuwar farashin lantarki ya karu a sassan Najeriya, daidai lokacin da hukumar lantarkin ke sanar da karuwar mutanen da ke amfani da mita.

Cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa-hannun shugabanta Farouk Ahmed ta bukaci kara farashin gas din da ake sayarwa kamfanonin rarraba lantarki daga farashin dala 2 da centi 18 kan kowanne cubic zuwa dala 2 da centi 42.

Kazalika sanarwar ta nemi kara farashin gas din da ake sayarwa daidaikun jama’a zuwa dala biyu da centi 92 daga dala 2 da centi 50 da ake sayarwa a baya.

A cewar Farouk, matakin da hukumar ta dauka ya yi daidai da tanadin sashe na 167 na dokar masana’antar man fetur ta shekarar 2021 da ta sahale bibiyar farashin da kuma sauya shi lokaci zuwa lokaci da kuma banbanta farashin da ake sayarwa kamfanonin na lantarki da daidaikun jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.