Isa ga babban shafi

Tsarin kara yawan jarin bankuna da CBN ya yi a Najeria na iya zuwa da kalubale

Shugaban kwamitin kula da hada-hadar jari na majalisar dattawan Najeriya Sanata Osita Izunazo ya ce da yiwuwar karin jarin bankuna zuwa nera biliyan 200 kan zo da irin nasa kalubalen.

Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja.
Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da kasuwar jari, Sanata Osita Izunaso, ya ce adadin kudin karfin jarin bankuna da aka kayyade bazai rasa irin nasa kalubale a wasu bangarori ba, musamman idan bankunan suka zabi hanyar sanya hannun jari masu zaman kansu.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne babban bankin Najeriya ya sanar da sabbin ka'idoji kan manufofinsa na mayar da hannun jari ga bankuna, inda ya umarci bankunan kasuwanci da ke da izinin kara yawan kudadensu zuwa Naira biliyan 500, da kuma bankunan kasar Naira biliyan 200.

Izunazo, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya bayyana cewa, ya kamata CBN ya kara zage damtse wajen ganin cewa ba a yi amfani da kudaden da aka wawashe ba wajen mayar da hannun jarin bankunan, kuma mutanen da suka dace ne kawai za su zama masu hannun jari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.