Isa ga babban shafi

Akwai yiwuwar maniyyatar Najeriya ba za su samu damar sauke farali a bana ba

A Najeriya, Majalisar Koli Tabbatar da Sharia''r Musulunci ta bayyana damuwa a game da barazanar  da aikin Hajjin bana ke fuskanta, biyo bayan labarin da ke cewa akwai yiwuwar maniyyatar kasar ba za su samu damar sauke farali a bana ba.

Kasa mai tsarki, Saudiya
Kasa mai tsarki, Saudiya REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

Binciken da majalisar ta gudanar kan shirye-shiryen aikin Hajjin na bana ya nuna akwai wagegen giɓi a game da shirye-shiryen.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar, wadda ta samu sa hannu sakatarenta, Nafiu Baba Ahmed ta ce wa'adin da hukumomin Saudiyya suka ɗiba game da kammala  shirye-shiryen da suka kamata, kama daga biyan kuɗin kujera zuwa sauran shirye shirye, na  iya cika ba tare da maniyyatan  sun san halin da suke ciki ba na ainihin kuɗin da ya kamata su cika kan kujerar.

Kasa mai tsarki Saudiya
Kasa mai tsarki Saudiya © REUTERS - Ahmed Yosri

Majalisar ta ce har ya zuwa wannan lokacin  ba a biya kuɗin rabin kujerun da aka ba wa Najeriya ba.

Daga bisani majalisar ta ce tana sane da irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen samun sauki musamman kan batun canjin dala wanda shi ne musabbabin wannan matsalar.

Mahajata a kasar Saudiya
Mahajata a kasar Saudiya AP - Amr Nabil

Ta kuma buƙaci 'yan siyasa da masu hannu  da shuni da kuma masu ruwa da tsaki da su taimaka yadda ya kamata domin ganin ba a samu koma baya a aikin Hajjin bana ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.