Akwai yiwuwar dubban maniyyata aikin Umrah su rasa damar shiga Saudiyya daga Najeriya
Majalisar koli ta tabbatar da shari'a ta tabbatar da shari'a a Najeriya na fargabar za a fuskanci tasgaro a bangaren masu niyyar aikin Umrah na wannan shekara, saboda irin matakan da mahukuntan Saudiyya suka dauka wajen samar da bizar shiga kasar
Wallafawa ranar:
Majalisar kolin tabbatar da shari’a ta Najeriya ta bayyana damuwar ta akan yiwuwar dubban maniyyata daga Najeriya su rasa damar zuwa Umrah a cikin watan ramadanan shekarar nan saboda matakin da hukumomin saudiya suka dauka na dakatar da bayar da biza
Yanzu haka mutane na cigaba da bayyana damuwarsu da batun musamman ganin cewa azumi na ta tafiya, idan Allah ya kai mu da rai da lafiya nan ba da jumawa ba za a kai ga rabin azumin.
Toh bayaga haka akwai yiwuwar hukumomin dake kula da harkokin hajj da Umrah su yi hasara ta kudade mai dinbin yawa bisa kama otel otel din da suka yi wa maninyata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu