Isa ga babban shafi
RAHOTO

Maniyyatan Najeriya 45,000 ne ba za su halarci aikin Hajji bana ba

Shugaban hukumar Alhazan Najeriya Malam Jalal Arabi ya umarci Sakatarorin Ofishin Hukumomin Alhazan Jihohi da su hada hannun da Malamai da Sarakuna wajen wayar da kan maniyata kan Muhimmanci sauke farali, sakamakon fargabar da ake da ita cewa, kusan kashi 89% na maniyatan Najeriyar ba za su samu damar sauke farali ba.  

Masana dai na ganin rashin maniyyatan baya rasa nasaba da tsadar kudin da aka samu daga hukumomin Najeriyar.
Masana dai na ganin rashin maniyyatan baya rasa nasaba da tsadar kudin da aka samu daga hukumomin Najeriyar. © PremiumTimes
Talla

Haka zalika, alamu sun nuna cewa kimanin ‘yan Najeriya 45,000 da suka biya kudin aikin hajjin 2023 ka iya zuwa kasar Saudiyya saboda matsalar biza.

A makwanni biyu da suka gabata maniyyata da dama sun kasa samun biza sakamakon tsaikon da hukumar Alhazai ta kasar NAHCON ta yi na tura kudaden aikin hajjin zuwa babban bankin Najeriya CBN.

Saboda haka, CBN ya kasa tura kudaden zuwa ga hukumomin alhazai da asusun ajiyar banki na masu yawon bude ido a Saudiyya don biyan kudin aikin hajji.

Domin sauraron cikakken rahoton, shiga alamar sauti.....

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.