Isa ga babban shafi

Najeriya ta rasa Mahajjata biyar a Saudiya

Hukumar kulada aikin Hajji ta Najeriya, ta tabbatar da mutuwar alhazanta biyar a kasar Saudiya a lokacin aikin hajjin bana.

Wani mahajjacin Najeriya a birnin Makkah.
Wani mahajjacin Najeriya a birnin Makkah. AFP PHOTOS / MARWAN NAAMANI
Talla

Shugaban bangaren kulada lafiyar hukumar Usaman Galadima ne ya bayyana haka, a lokacin taron da hukumar ta gudanar a birnin Makkah, inda ya ce yanzu haka akwai wasu mutum 30 da ke fama da rashin lafiyar kwakwalwa.

Ya ce jahohin Osun da Kaduna ke da mahajjata biyu-biyu da suka rasu, ya yinda jahar Filato ke da mahajjaci daya.

Galadima ya ce marasa lafiyar na samun kulawar da ta kamata a cibiyar kulada lafiya ta kasar, kuma ana saran za su gudanar da aikin Hajji.

Har wayau, Galadima ya ce mahajjata mata biyu sun yi bari, sannan kuma wata mahajjaciyar Najeriya ta haihu a aikin hajjin bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.