Isa ga babban shafi
TALLAFI

Raba kudaden tallafi ya tada kura a majalisar dattawan Najeriya

Najeriya – Wani ‘dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Jarigbe Jarigbe ya yi zargin cewar shugabannin majalisar na nuna son kai wajen raba kudaden tallafin da aka warewa kowacce mazaba a kasar.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio kenan.
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio kenan. © PremiumTimes
Talla

Jarigbe yace yayin da wasu daga cikin su suka karbi naira miliyan 200, wasu shafaffu da mai sun karbi naira miliyan 500 ne domin tallafawa mazabun su.

Rahotanni sun ce yayin mahawara a kan zargin da Sanata Ningi ya yi, ‘dan majalisar dattawa Jarigbe ya bayyana cewar lalle akwai wasu shafaffu da mai a tsakanin ‘yan majalisun, ganin yadda aka raba wadannan kudaden na tallafi a tsakanin su.

Sanata Jarigbe yace abin takaici ne, yayin da wasu ‘yan majalisun suka karbi naira miliyan 500 a matsayin tallafin mazabun su, wasu kuma an basu naira miliyan 200 ne kacal.

Firta wadannan kalamai ya sake jefa majalisar cikin rudani, inda wasu ‘yan majalisar suka yiwa Sanata Jarigbe caa saboda kalaman na sa.

Ya zuwa wannan lokaci dai babu wani gamsashen bayani daga shugabancin majalisar dangane da wannan zargi na fifita wasu ‘yan majalisu wajen raba kudaden tallafin.

Ga alama dai ana iya cewar har yanzu tsuguni bata karewa wannan Majalisar ba, a daidai lokacin da ta ke kokarin kashe wutar da Sanata Abdul Ningi ya kunna dangane da zargin sanya wasu makudan kudade a cikin kasafin kudin bana ba bisa ka’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.