Isa ga babban shafi

Lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta cire tallafin lantarki - IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF, ya shawarci gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da ta cire tallafin lantarki gaba daya, duk da cewa ‘yan kasar na kokawa da tsadar rayuwa, bayan tallafin mai da gwamnatin ta cire a watan Mayun 2023.

Kasar dai na fama da katsewar lantarki, daidai lokacin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa da kuma man fetur.
Kasar dai na fama da katsewar lantarki, daidai lokacin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa da kuma man fetur. REUTERS - AKINTUNDE AKINLEYE
Talla

A cewar wani rahoto da IMF ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, y ace gwamnatin Najeriya tana tursasa kanta kan abubuwan da suka neman fin karfinta, don haka akwai bukatar ta janye tallafin lantarki kamar yadda ta cire na man fetur.

Cibiyar ta Bretton Woods ta bayar da wannan shawarar a matsayin hanyar da Najeriya za ta bi domin farfado da tattalin arzikin kasar da ya shiga wani hali, abin da ke zuwa daidai lokacin da gwamnatin kasar ta ce tallafin wutar lantarki tsakanin watan Janairu zuwa Satumban 2023 ya lakume Naira biliyan 375.8, yayin da masu amfani da wutar lantarki suka biya jimillar naira biliyan 782.6.

IMF ya yabawa gwamnatin Najeriya kan sauye-sauyen da ta aiwatar zuwa yanzu amma ta sake nanata cewa ya kamata a cire tallafin lantarki kamar yadda aka cire a bangaren man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.