Isa ga babban shafi

Bayan kwato bashin noma bankin Najeriya ya fara karbo rancen Covid-19

Bayanai daga Najeriya na cewa babban bankin kasar CBN ya fara aiwatar da matakin karbo rancen da ya baiwa wasu ‘yan kasar domin saukaka musu radadin kuncin tattalin arzikin da barkewar annobar Korona ta haddasa a sassan duniya.

Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja.
Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN da ke birnin Abuja. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Bankin Najeriyar dai ya bayar da tallafin rancen ne a tun shekarar 2020.

Bayanai sun ce tuni bankin na CBN ya fara cire kudaden da yake bin wasu da ya bai wa rancen daga asusunsu, sai dai wasu na korafi akan tsarin da ake bi wajen karbar kudaden, inda a maimakon a rika janye musu kudaden a hankali, sai a rika zaftare jimillar adadin kudaden tallafin da suka amfana da shi a lokaci guda, abinda suka ce yana matukar jefa su a cikin kuncin gurguncewar gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Wani batu kuma da a yanzu yake daukar hankali shi ne alwashin da gwamnatin Najeriya ta yi na kammala karbo tallafin rancen kudaden da ta bai wa dubun dubatar manoman kasar a karkashin shirin ‘Anchor Borrower’ da aka fara a shekarar 2015, domin inganta ayyukan noma.

A wannan Litinin ne dai wa'adin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kayyade na tabbatar da cewa an karbo bashin noman daga wadanda suka amfana ya cika.

Babban bankin Najeriya ya ce zuwa shekarar 2022, manoma akalla miliyan 4 da dubu 800 ne suka samu  tallafin shirin bunkasa noman na ‘Anchor Borrower’, sai dai akasarin wadanda suka amfana da tallafin rancen basu  mayar da kudaden ba, duk kuwa da cewar farashin albarkatun gonar da suka noma ya karu sosai.

Wani rahoton asusun ba da lamuni na duniya IMF ya nuna cewar, kashi 76 cikin 100 na adadin kudaden rancen da bankin CBN ya bai wa monama a Najeriyar ne ba a maida ba.

Wannan ce ta sanya sabon shugaban Najeriya shan alwashin kawo karshen matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.