Isa ga babban shafi

Mutane dubu 4 da 486 sun mutu a rikice-rikice 15 daga 1994 zuwa 2023 a Filato

Wasu alkaluma da jaridar Preimium Times a Najeriya ta tattara game da adadin mutanen da suka mutu a mabanbantan rikicin kabilanci 15 da suka faru a jihar Filato ta tsakiyar kasar daga shekarar 1994 zuwa yanzu, sun nuna yadda akalla mutane dubu 4 da 486 suka rasa rayukansu a sassan jihar.

Yadda wani hari ya salwantar da rayukan tarin mutane a jihar Pulato ta Najeriya.
Yadda wani hari ya salwantar da rayukan tarin mutane a jihar Pulato ta Najeriya. AP - APTN
Talla

Tun farko hukumar samar da zaman lafiya a jihar Filato ta Plateau Peace Building Agancy ce ta fitar da alkaluman yawan mutanen da suka mutu a rikice-rikicen da jihar ta gani daga shekarar 1994 zuwa 2021.

Ko watan jiya wani sabon rikicin kabilancin ya sake barkewa a karamar hukumar Mangu ta jihar ta Filato wanda ya haddasa asarar dimbin rayuka da dukiyoyi yayinda wasu da dama suka jikkata a bangare guda aka kone tarin gidaje ciki har da wuraren ibada.

Haka zalika a jajiberan ranar Kirsimati an ga yadda wasu hare-haren ‘yan bindiga suka kai ga kisan mutane fiye da 100 a kauyukan Barkin Ladi da karamar hukumar Bokkos.

Ko a watan Aprilun bara sai da fiye da mutane 300 suka mutu a wani rikicin kabilanci a karamar hukumar Mangu ta jihar baya ga barnata tarin dukiyoyin, rikicin da aka shafe watanni aka kaiwa juna farmaki.

Bangarorin da ke rikicin dai na zargin juna da daukar sojin haya don taya su rikicin inda zuwa yanzu aka samu manyan rikici har 15 cikin shekarun 30 da ya haddasa asarar dimbin rayuka.

A ranar 12 ga watan Aprilun 1994 ne rikicin farko ya fara barkewa a jihar ta Filato biyo vayan nadin Alhaji Mato wani bahaushe a matsayin babban jami’in gwamnati a karamar hukumar Jos ta arewa, lamarin da ‘yan kabilar Berom da Anaguta da kuma Afizere suka ki amincewa da shi tare da tayar da rikici, gabanin gwamnati ta gaggauta janye nadin.

A shekarar 1995 wani sabon rikicin ya kare barkewa tsakanin kabilun Mwaghavuls a Mangu da Ron a Bokkos gabanin makamancinsa a 1997 tsakanin Hausawa da Berom wanda shi ne karon farko da aka fara samun asarar rayuka.

A shekarar 2001 ne rikicin ya tsananta a Filato wanda ake sanyawa a sahun mafiya muni da jihar ta gani, inda mutane fiye da dubu guda suka mutu wasu suka bace dukiyoyi suka salwanta aka kuma kone gidajen wasu, shi ma dai akan nadin mukami.

A shekarar 2002 sabon rikici ya sake barkewa wanda ya haddasa asarar akalla rayukan mutum 600 yayinda wani makamancinsa ‘yan watanni tsakani ya sake lakume rayukan fiye da mutum 100 a Angwan Rukuba da Nasarawa Gwom da kuma Yelwa Shendam.

Duk dai a shekarar wani rikici da ya barke cikin daren ranar 26 ga watan Yuni ya kai ga asarar akalla rayukan mutane 500.

A shekarar 2004, an ga yadda aka yiwa musulmi kusan 700 kisan gilla cikin watan Mayu a Yelwan Shendam yayinda a 2008 wani rikici bayan zaben kananan hukumomi ya hallaka mutane akalla dubu guda galibinsu Hausawa.

Alkaluman sun nuna yadda 2010 wasu mutum 400 suka mutu bayan rikicin addini a yankin Nasarawa da ke Jos ta arewa sai kuma wasu 300 a watan Maris.

Ko a shekarar 2011 rikicin siyasa tsakanin magoya bayan jam’iyyar CPC da PDP ya kai ga asarar rayuka sai kuma rikicin makiyaya da manoma a 2016 cikin watannin Fabarairu da Yuli da kuma Satumba ya haddasa asarar dimbin rayuka.

A shekarar 2018 wani rikicin ya sake hallaka mutane 57 a kauyen Dura Du wanda ya ritsa da babban Sojin Najeriya Idris Akali, yayinda a 2020 da 2021 wasu mutane 30 da 80 suka mutu a hare-haren sari ka noke da kabilu ke kaiwa junansu a Irigwe da Bassa da Riyom da Barikin Ladi.

Haka zalika wasu mutane 58 sun rasa rayukansu a rikicin makiyaya cikin shekarar 2022 yayinda wasu fiye da 400 suka mutu a 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.