Isa ga babban shafi

Fiye da mutane 100 sun mutu cikin sa'o'i 48 a hare-haren jihar Filato- Maren

Wasu bayanai na nuna cewa cikin sa’o’I 48 hare-haren ‘yan ta’adda ya kashe mutanen da yawansu ya haura 100 a wasu sassa na jihar Filato dai dai lokacin da gwamnatin jihar ta sanya dokar takaita walwalar jama’a a yankunan da hare-haren ke faruwa.

Yadda wani hari ya salwantar da rayukan tarin mutane a jihar Pulato ta Najeriya.
Yadda wani hari ya salwantar da rayukan tarin mutane a jihar Pulato ta Najeriya. AP - APTN
Talla

Dan Majalisar tarayya da ke wakiltar Mangu da Bokkos Solomon Maren yayin jawabinsa gaban zaman zauren majalisar jiya laraba, ya ce mahara na ci gaba da kai hare-hare kan kauyuka tare da kisan mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Mr Maren, ya bayyana cewa hare-haren sun fi tsananta a yankin da ya ke wakilta a jihar ta Filato da ke tsakiyar Najeriya wanda ke nuna bukatar daukar mataki lura da yadda mutanen kauyukan da ake kai hare-haren ke rayuwa cike da fargaba.

Dan Majalisar ya bayyana cewa cikin sa’o’I 48 sai da hare-haren ya kashe mutane fiye da 100 wanda ke nuna mutuwar mutanen da yawansu yah aura 200 a makamantan hare-haren cikin watanni 2 da suka gabata.

A cewar Mr Maren maharan na kone gidaje da gonaki har ma da shagunan da ake adana amfanin gona yana mai kakkausar suka ga matakan da gwamnati ke dauka a kokarin yaki da matsalar tsaron da yankuna da dama ke fama da shi a Najeriya.

Matsalar tsaro na ci gaba da ta'azzara a sassan Najeriya musamman yankin arewaci inda 'yan bindiga ke kai hare-haren ba gaira babu dalili tare da kisan tarin mutane da kuma sace dukiyoyinsu.

Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Tasiu Zakari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.