Isa ga babban shafi
Najeriya - Buhari

Buhari ya roki al'ummar Jos da su rungumi zaman lafiya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya roki al'ummar Filato su rungumi zaman lafiya, tare da jaddada cewa gwamnatin na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo karshen duk wani tashin hankali.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya karbi bakwanci gwamnan jihar Filto Simon Lalong a fadar gwamnati dake Abuja 24/08/21.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya karbi bakwanci gwamnan jihar Filto Simon Lalong a fadar gwamnati dake Abuja 24/08/21. © femi adeshina
Talla

Shugaban ya yi kiran ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, inda ya jaddada samun nasara tare da bukatar al’ummomin yankin su hada kai don yakar bata gari, yana mai cewa tashin hankali ba zai zama mafita ba.

Sanarwar ta ce duk da irin kokarin da gwamnati take yi wajen tabbatuwar zaman lafiya, bai kamata malaman addinai da sarakuna da sauran shugabannin al’umma su bari ana yada tashin hankali da tunzura jama’a ba.

Tarin matsaloli

Buhari ya ce akwai tarin matsalolin da kasar ke fama a yanzu kuma yana da muhimmanci 'yan Najeriya da sauran kasashe su fahimci kokarin da suke yi wajen kawar da duk wasu rigingimu a fadin kasar.

Wannan na zuwa ne yayin da Gwamnan Jihar Plateau Simon Bako Lalon ya ziyarci Yelwa Zangam inda aka kashe mutane sama da 30 a makon jiya inda ya gana da Basaraken Yankin da kuma mutanen da suka rasa Yan uwan su.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya karbi bakwanci gwamnan jihar Filto Simon Lalong a fadar gwamnati dake Abuja 24/08/21.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya karbi bakwanci gwamnan jihar Filto Simon Lalong a fadar gwamnati dake Abuja 24/08/21. © femi adeshina

Bayan ziyarar mun tuntubi kwamishinan yada labarai Dan Manjang kuma ga jawabin da yayi mana akai, kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren abin da yake cewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.