Isa ga babban shafi
Nigeria - Filato

'Yan sanda sun cafke mutane 6 kan kisan da aka yiwa matafiya a Filato

Gwamnatin Filato da ke Najeriya ta kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a yankunan kananan hukumomin Bassa, Jos ta Arewa da kuma Jos ta Kudu, domin tabbatar da tsaron rayukan jama’a, biyo bayan kashe wasu matafiya 22 da ‘yan bindiga suka yi.

Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya.
Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya. AFP
Talla

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta sanar da cafke wasu mutane 6 bisa zargin suna da hannu a farmakin na ranar Asabar, bayan da ta zargi matasan kabilar Irigwe da yiwa matafiyan kisan gilla a yankin Gada-Biyu da ke hanyar Jos zuwa Zaria a karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar ta Filato.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin kan ayarin matafiya daga wani taron addini a Bauchi, akan hanyar Jos babban birnin jihar Filato.

Cikin sanrwar da ya fitar a daren ranar Asabar, kakakin shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu, ya ce tuni Buhari ya bada umarnin farautar wadanda ke da hannu cikin ta’addancin don gurfanar da su a gaban shari’a.

Fadar shugaban Najeriyar ta kuma yaba da kokarin da gwamnonin Filato, Bauchi, da Ondo ke yi; tare da hadin gwiwar Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, da Sheikh Dahiru Usman Bauchi da kuma wasu fitattun shugabannin Kiristoci da Musulmai don don kwantar da hankulan jama’a kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.