Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana fargabar rasa rayuka da dama a sabon harin da aka kai a Jos

Rahotanni daga jihar Filato sun ce an kashe mutane da dama, tare da kone gidaje a Yelwan Zangam da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.

Wani bangare na arewa maso gabashin garin Jos.
Wani bangare na arewa maso gabashin garin Jos. © Wikipedia
Talla

Harin na zuwa ne kusan mako guda bayan da aka kashe matafiya fiye da 20 a hanyar Gada-biyu. zuwa Rukuba, a dai karamar hukumar ta Jos ta Arewa.

Wakilinmu da ke garin Jos ya tabbatar mana da aukuwar tashin hankalin, inda ya ce ana fargabar akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu, kodayake babu tabbas kan ko adadin ya kai hakan ko kuma ya zarce.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labari dai Rundunar 'yan sandan jihar Filato ba ta bayar da cikakken bayani kan aukuwar lamarin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.