Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

‘Yan bindiga sun sace matar wani kwamishinan Filato da 'Yarsa

A Najeriya, ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan Kwamishinan Muhalli na Jihar Filato, Usman Bamaiyi, a safiyar wannan Asabar, inda suka yi awon gaba da matarsa da ‘yarsa.

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Babu tabbas ko kwamishinan yana gida ne lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan da ke unguwar Gindiri a karamar hukumar Mangu ta jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni jami’an rundunar suka bi sahun wadanda suka sace su domin ganin an ceto su da kuma kubutar da mutanen.

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da aka sace wasu fastoci biyu a yankin.

Harin na Filato ya zo ne kasa da mako guda bayan wasu ‘yan bindiga sun harbe dan wani kwamishina mai ci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.