Isa ga babban shafi
Najeriya-Jos

'Yan bindiga sun kubutar da fursunoni 250 a Jos

Akalla mutane 11 aka kashe, sannan fiye da fursunoni 250 suka tsere bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani gidan yari da ke birnin Jos na jihar Filato ta Najeriya.

Fursunoni 250 suka tsere daga gidan yarin na Jos
Fursunoni 250 suka tsere daga gidan yarin na Jos Pius Utomi Ekpei AFP/Archivos
Talla

Harin da aka kaddamar a ranar Lahadin da ta gabata, shi ne na baya-bayan nan da ya yi sanadiyar tserewar fursunoni a Najeriya, kasar da ke zama mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika, inda ake yawan samun cinkoson gidajen yari.

Mai magana da yawun gidan yarin na Jos, Francis Enobore ya ce, an kashe fursunoni 9 da mahari guda da kuma jami’in tsaro guda bayan ‘yan bindigar sun kai farmakin, yayin da fursunoni 262 suka arce.

Ku latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren rahoton wakilinmu Tasi'u Zakari.

 

03:07

'Yan bindiga sun kubutar da fursunoni 250 a Jos

 

An dai yi nasarar sake kama fursunoni 10 jim kadan da kawo karshen harin wanda ya janyo musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da jami’an tsaro.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan jihar Filato, Ubah Ogaba ya ce, an sake cafke mutanen tara, yayin da wani guda ya mika kansa da kansa ga hukumomi.

An kai harin ne a daidai lokacin da gidan yarin ke dauke da fursononi dubu 1 da 60.

Wannan na zuwa ne bayan sama da fursunoni 800 sun arce daga gidan yarin Abolongo da ke jihar Oyo ta yankin kudu maso yammacin Najeriya a watan jiya, inda ‘yan bindiga suka fasa gidan yarin da wasu abubuwan fashewa.

Kodayake an kama fiye da rabinsu a washe-garin aukuwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.