Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya sun kaddamar da wani shirin dakile kashe-kashen jihar Filato

Sojin Najeriya ta kaddamar da wani runduna ta musamman domin kawo karshen kashe kashen jihar Filato, wanda aka yi wa lakabi da Hakorin Damisa ta 4.

Sojin Najeriya ta kaddamar da wani runduna ta musamman domin kawo karshen kashe kashen jihar Filato, wanda aka yi wa lakabi da Hakorin Damisa ta 4. 22/07/22.
Sojin Najeriya ta kaddamar da wani runduna ta musamman domin kawo karshen kashe kashen jihar Filato, wanda aka yi wa lakabi da Hakorin Damisa ta 4. 22/07/22. © Nigerian Army - Twitter
Talla

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya kaddamar da sabuwar rundunar wannan asabar a karamar hukukumar Mangu ta jihar domin kawo karshen hare-hare da kisan jama’a ba gaira babu dalili a Mangu da wasu sashi na jihar baki daya.

Sojin Najeriya ta kaddamar da wani runduna ta musamman domin kawo karshen kashe kashen jihar Filato, wanda aka yi wa lakabi da Hakorin Damisa ta 4. 22/07/23.
Sojin Najeriya ta kaddamar da wani runduna ta musamman domin kawo karshen kashe kashen jihar Filato, wanda aka yi wa lakabi da Hakorin Damisa ta 4. 22/07/23. © Nigerian Army - Twitter

Rikicin baya-bayan nan a yankin ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 300 a karamar hukumar Mangu da kewaye cikin watanni biyu sakamakon hare-hare mabanbanta da ‘yan bindiga suka kai.

Bayan kaddamar da sabuwar rundunar ta Hakorin Damisa, shugaban sojin kasa na Najeriyar ya kuma yi wata ganawar sirri da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar a wata makarantar firamare dake garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.